Labarai
Sakataren Gwamnatin Kano Ya Ja Hankalin Manema Labarai Kan Fitar Da Sahihan Labarai
Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya bukaci manema labarai da su kara jajircewa a sha’anin aikin su musamman a daidai wannan lokaci da babban zaben shekarar 2027 ke kara karatowa.
Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya bayyana haka ne yayin taron kara wa juna sani da kungiyar wakilan kafafen yada Labarai na kasa reshen jihar Kano ta shirya a jihar Kaduna.
Ya ce a daidai wannan lokaci manema labarai suna da muhimmiyar rawar da za su taka domin tabbatar da samun sahihi Kuma ingantaccen zaben shekarar 2027 da ke kara karatowa a halin yanzu.
Sakataren gwamnatin Wanda sakataren yada labaran fadar Gwamnatin jihar Kano Malam Mustafa Muhammad ya wakilta ya bayyana yadda manema labarai ke taka rawa a sha’anin inganta rayuwar Al’uma baki Daya.
Dangane da rawar da manema labarai ke taka wa dangane da ayyukan gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya bayyana haka a matsayin shaidar gani da ido bisa yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke bujiro da ayyukan raya kasa a sassa daban-daban na jihar Kano.
Sakataren gwamnatin na jihar Kano ya kara da cewa aikin yada Labarai ba yana nufin mayar da hankali wajen yada labarai marasa inganci ba ne, Sai dai fito da abubuwan da za su kara Fadakar da Al’uma Kan yadda gwamnati ke aiwatar da ayyukan raya kasa a ko’ina musamman a fannin Ilmi da lafiya da aikin Gona da cigaban Matasa ta hanyar bai wa Matasa jarin sana’o’i domin dogaro da Kan su.
Da yake jawabi, kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna Alhaji Ahmad Maiyaki ya bayyana muhimmancin ayyukan yada labarai a jihar Kano wacce ke Kan gaba a sha’anin siyasar yankin Arewacin kasar nan.
Sauran wadanda suka yi jawabi yayin taron akwai kwararre a bangaren yada labarai ta hanyar fasahar sadarwa Abdullatif Abubakar Jos da Barrister Yusuf Abdussalam da Kuma wakili daga Hukumar Zabe ta kasa.
Sauran manyan da Suka halarci taro akwai Shugaban kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen jihar Kano comrade Sulaiman Abdullahi Dederi Wanda mataimakinsa Comrade Mustafa Gambo Muhammad ya wakilta da takwaransa na jihar Kaduna Comrade Abdul Gaffar Alabalewa da me bai wa gwamnan Kano shawarar Kan kafafen yada Labarai ta hanyar fasahar sadarwa Malam Ibrahim Adam.
Labarai
Karamar hukumar Tarauni Kaddamar Da Rabon Gyadar Yara A Asibitocin Yankin
Karamar hukumar Tarauni Kaddamar Da Rabon Gyadar Yara A Asibitocin Yankin
Daga Adamu Ilyasu Hotoro.
Karamar hukumar Tarauni ta kaddamar da rabon Gyadar Yara sama da katan 66 a Asibitocin Yankin domin Kare Kananan yara daga cutar yunwa.
Jami’ar kula da abinci mai gina jiki a Ƙaramar Hukumar Tarauni, Hajiya Nafisa Sale Arab, ita ce ta bayyana cewa tuni aka raba kwalaye fiye da 66 na Gyadar tamowa ga wasu asibitoci dake cikin ƙaramar hukumar, domin taimaka wa yaran da ke fama da matsalar ciwon yunwa a yankin.
Hajiya Nafisa ta bayyana hakan ne a lokacin da take rabon Gyadar a Asibitin Dantsinke da Asibitin Yara na Isiyaka Rabiu, dake kan titin Zoo Road a cikin Ƙaramar Hukumar Tarauni.
Nafisa sale ta bayyana cewa kowanne daga cikin asibitocin biyu ya samu kwalin 33 na gyadar tamowar domin kula da yaran da ke fama dake da matsala ciwon yunwa
A cewar jami’ar da ke kula da sashin abinci mai inganci ta ce wannan tallafi na da nufin tabbatar da cewa yaran da ke fama da ciwon tamowa sun samu abincin da ya dace domin taimaka musu wajen samun sauƙi da inganta lafiyarsu.
Haka kuma, ta jaddada muhimmancin samar da ingantaccen abinci ga yara, musamman waɗanda ke fama da matsananciyar ciwon tamowa, domin taimaka musu wajen murmurewa cikin sauki.
Ana sa ran kowanne yaro mai fama da ciwon tamowa duk sati zai amfana da gyada 14 wanda duk Wata yaro daya zai shanye kwali daya na gyadar da aka samar domin kula da yaron da suke da bukata domin gina lafiyar jikinsu ta ce wannan gyadar ta watan October zuwa December ce aka raba na wannan shekarar da muke ciki.
Daga nan ta yaba wa Gwamnan jihar Kano da ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar kula da lafiya a matakin farko da kuma karamar hukumar Tarauni da hukumomin lafiya na duniya WHO,m da UNICEF da sauran sauran su bisa yadda suke bayar kyakyawan hadin Kai da goyen baya ake Samun nasarar gudanar da aikin a kowanne lokaci.
Labarai
Karamar Hukumar Tarauni Ta Raba Kayan Karatu Kyauta Ga Daliban Primary 9,500
Karamar Hukumar Tarauni Ta Raba Kayan Karatu Kyauta Ga Daliban Primary 9,500
Daga Adamu Iliyasu Hotoro, ANIPR
Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya ƙaddamar da rabon kayan makaranta kyauta ga ɗaliban makarantun firamare guda 9,500, a matsayin tallafi daga Gwamnatin Jihar Kano domin inganta harkokin ilimi da sauƙaƙa wa iyaye domin a rage musu nauyin karatu ga ’ya’yansu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Alhaji Ahmed Ibrahim shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ƙaddamar da rabon kayan makarantar tare da shugabannin makarantun firamare da ke yankin a harabar sakatariyar karamar hukumar Tarauni.
Ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin injiniya Abba Kabir Yusif na inganta harkokin ilimi da samar da kayan karatu ga ɗalibai domin ƙarfafa musu gwiwar zuwa makaranta da samun ingantaccen ilimi.
A jawabinsa tun da fari shugaban sashin illimi na Karamar hukumar Tarauni Kwamared Bashir Muhammad Karkasara ya yaba wa shugaban karamar hukumar Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure da Gwamnan Jihar Kano bisa wannan tallafi, yana mai bayyana cewa samar da kayan makaranta ga ɗalibai zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan iyaye da magance matsalar yaran da basa san zuwa makaranta.
Ya kuma buƙaci shugabannin makarantun da su tabbatar da cewa an raba kayan ga ɗaliban da suka cancanta, tare da yin amfani da su yadda ya kamata domin cimma nasarar da aka sa a gaba.
A jawabinsa Daraktan Mulki da gudanarwa na karamar hukumar Alhaji Tijjani Madaki Gulya ya jaddada aniyar na cigaba da da bawa shugaban karamar hukumar ta Tarauni shawara wajan kara bunkasa Sashen Ilimi na Ƙaramar Hukumar musanman wajan hada gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki wajen cigaba da inganta harkokin ilimi da samar da kyakkyawan makoma ga ɗalibai a matsayin su na manyan gobe.
Labarai
Kungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano
Kungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano
Kungiyar masu shaguna a filin Idi da ke Unguwar Kofar Mata cikin karamar hukumar birnin Kano ta gudanar da addu’oi na musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi II bisa kokari wajen dawo musu da shagunan su da gwamnatin jihar Kano ta rushe shekaru 3 da suka gabata.
Shugaban kungiyar Alhaji Abbas sa’id Umar jim kadan bayan kammala taron addu’ar ya bayyana cewa sun kammala Saukar karatun Alkur’ani sai 111 da Kuma karanta Hasbunallahu Wani’imal Wakil sau Dubu 111 ga wadannan shuganni guda 2 bisa kokarin dawo musu da wadannan shagunan domin cigaba da kasuwancin su.
” Tun bayan rushe mana shaguna Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi II ya rubuta takarta ga gwamnatin jihar Kano na a dube mu. Kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya saurari wannan koke Kuma ya yi alkawarin kawo mana dauki.” In ji Alhaji Abbas sa’id Umar
Shugaban kungiyar ya kara da cewa tun bayan rushe shagunan da ke cikin Masallacin na Idi wasu daga cikin wadanda aka rushe wa shagunan sun rasu, wasu Kuma sun kamu da rashin lafiya, wasu kumu Jarin su ya karye.
” Muna kara mika kokon barar mu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya kawo mana dauki bayan tabbatar mana da wannan wuri da Kuma tallafa mana bisa wannan hali da muke ciki.” In ji Alhaji Abbas sa’id Umar
Shugaban kungiyar ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa amincewa da dawo mana da wani yanki daga wuraren da aka rushe mana.
” Shagunan sun kai 700 da aka rushe, amma cikin ikon Allah gwamnatin jihar Kano ta amince da samar shaguna 75 da Kuma Karin wasu a nan gaba ga mutanen mu domin ciga da kasuwancin su.” In ji Shugaban kungiyar
Da yake Karin haske yayin taron, Farfesa Ibrahim Mu’azzam Mai Bushra ya yaba wa gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan halin tausayi ga wadannan masu shaguna da aka rushe wa shagunan su shekaru 3 da suka gabata.
Shi ma Farfesa Ibrahim Ahmad Muhammad na Jami’ar Tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya bayyana sake Samar wa da ‘yan Kasuwar ta filin Idi da cewa zai kara inganta sha’anin kasuwancin jihar Kano da ma kasa baki Daya.
-
Labarai2 months agoGwamnatin Kano Ta Fitar Da Iyaka Tsakanin BUK Da Garin Rimin Zakara
-
Labarai1 week agoKungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano
-
Labarai1 week agoKungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano
-
Labarai1 week agoKaramar Hukumar Tarauni Ta Raba Kayan Karatu Kyauta Ga Daliban Primary 9,500
-
Labarai1 week agoKungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano
-
Labarai4 hours agoKaramar hukumar Tarauni Kaddamar Da Rabon Gyadar Yara A Asibitocin Yankin
