Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Iyaka Tsakanin BUK Da Garin Rimin Zakara

Published

on

  • Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Iyaka Tsakanin BUK Da Garin Rimin Zakara – Kwamishina Abduljabbar

Gwamnatin jihar Kano ta kammala fitar da Iyaka Tsakanin Jami’ar Bayero da yankin Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo bayan kawo karshen Takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ne ya bayyana haka yayin da ya jagoranci kaddamar da aikin fitar da iyakar a garin na Rimin Zakara a Karamar hukumar Ungogo.

Ya ce a wannan lokaci dukkanin Takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu ya kawo karshe kasancewar an fitar da Iyaka Tsakanin Jami’ar Bayero da Kuma sabon birnin da gwamnatin jihar Kano ta fitar wa da Al’umar yankin na Rimin Zakara.

” Daga yanzu duk wanda aka samu da laifin yanka filaye a wurin da aka ware wa Jami’ar Bayero, to ya tabbata Doka za ta yi aiki a Kan sa kasancewar duk masu korafi daga cikin Al’umar yankin suma gwamnatin jihar Kano ta sallame su ta hanyar biyan su Diyyar kudi da Kuma filaye a sabon birnin da aka fitar.” In ji kwamishina Abduljabbar

Kwamishina Abduljabbar Muhammad Umar ya kara da cewa da zarar an kammala fitar da iyakar gwamnatin jihar Kano za ta bai wa kowanne bangaren takardar shaida da za ta Kare duk wata barazanar cin Iyaka daga Bata-garin Dillalai.

Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya ja hankalin Al’uma Kan su kaucewa yin mu’amala bata-garin Dillalai wadanda su ne Suka haddasa wannan tashin tashina. Inda ya ce gwamnatin jihar Kano za ta Sanya kafar wando guda da duk irin wadancan Bata -garin Dillalai idan ta Kama su.

A jawabinsa wakilin Jami’ar Bayero a wurin farfesa Ahmad Muhammad Tsauni ya bayyana farin cikin su bisa wannan rana, inda ya ce Jami’ar Bayero ta fi kowa farin cikin kawo karshen wannan Takaddamar da ta dauki shekaru tsakanin su da Al’umar yankin na Rimin Zakara.

Shi kuwa Shugaban kwamitin Al’umar yankin da ya shiga tsakani domin samun Daidaito Alhaji Baba Habu yaba wa gwamnatin jihar Kano ya yi bisa cika alkawarin kawo karshen wannan Takaddamar da ta gagari gwamnatoci da yawa a baya.

” Ina tabbatar muku cewa tun lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora wa kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar nauyin cewa ya yi duk abin da ya dace domin kawo karshen Takaddamar. Babu wani lokacin da muka bukaci zama da kwamishinan ya ki amincewa duk kuwa da abubuwan da Suka faru na rashin Dadi daga mutanen yankin saboda fuwata da Suka yi a baya.” In ji Alhaji Baba Habu

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 7   +   3   =  

Labarai

Karamar Hukumar Tarauni Ta Raba Kayan Karatu Kyauta Ga Daliban Primary 9,500

Published

on

Karamar Hukumar Tarauni Ta Raba Kayan Karatu Kyauta Ga Daliban Primary 9,500

Daga Adamu Iliyasu Hotoro, ANIPR

Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya ƙaddamar da rabon kayan makaranta kyauta ga ɗaliban makarantun firamare guda 9,500, a matsayin tallafi daga Gwamnatin Jihar Kano domin inganta harkokin ilimi da sauƙaƙa wa iyaye domin a rage musu nauyin karatu ga ’ya’yansu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Alhaji Ahmed Ibrahim shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ƙaddamar da rabon kayan makarantar tare da shugabannin makarantun firamare da ke yankin a harabar sakatariyar karamar hukumar Tarauni.

Ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin injiniya Abba Kabir Yusif na inganta harkokin ilimi da samar da kayan karatu ga ɗalibai domin ƙarfafa musu gwiwar zuwa makaranta da samun ingantaccen ilimi.

A jawabinsa tun da fari shugaban sashin illimi na Karamar hukumar Tarauni Kwamared Bashir Muhammad Karkasara ya yaba wa shugaban karamar hukumar Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure da Gwamnan Jihar Kano bisa wannan tallafi, yana mai bayyana cewa samar da kayan makaranta ga ɗalibai zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan iyaye da magance matsalar yaran da basa san zuwa makaranta.

Ya kuma buƙaci shugabannin makarantun da su tabbatar da cewa an raba kayan ga ɗaliban da suka cancanta, tare da yin amfani da su yadda ya kamata domin cimma nasarar da aka sa a gaba.

A jawabinsa Daraktan Mulki da gudanarwa na karamar hukumar Alhaji Tijjani Madaki Gulya ya jaddada aniyar na cigaba da da bawa shugaban karamar hukumar ta Tarauni shawara wajan kara bunkasa Sashen Ilimi na Ƙaramar Hukumar musanman wajan hada gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki wajen cigaba da inganta harkokin ilimi da samar da kyakkyawan makoma ga ɗalibai a matsayin su na manyan gobe.

Continue Reading

Labarai

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano

Published

on

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano

Kungiyar masu shaguna a filin Idi da ke Unguwar Kofar Mata cikin karamar hukumar birnin Kano ta gudanar da addu’oi na musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi II bisa kokari wajen dawo musu da shagunan su da gwamnatin jihar Kano ta rushe shekaru 3 da suka gabata.

Shugaban kungiyar Alhaji Abbas sa’id Umar jim kadan bayan kammala taron addu’ar ya bayyana cewa sun kammala Saukar karatun Alkur’ani sai 111 da Kuma karanta Hasbunallahu Wani’imal Wakil sau Dubu 111 ga wadannan shuganni guda 2 bisa kokarin dawo musu da wadannan shagunan domin cigaba da kasuwancin su.

” Tun bayan rushe mana shaguna Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi II ya rubuta takarta ga gwamnatin jihar Kano na a dube mu. Kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya saurari wannan koke Kuma ya yi alkawarin kawo mana dauki.” In ji Alhaji Abbas sa’id Umar

Shugaban kungiyar ya kara da cewa tun bayan rushe shagunan da ke cikin Masallacin na Idi wasu daga cikin wadanda aka rushe wa shagunan sun rasu, wasu Kuma sun kamu da rashin lafiya, wasu kumu Jarin su ya karye.

” Muna kara mika kokon barar mu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya kawo mana dauki bayan tabbatar mana da wannan wuri da Kuma tallafa mana bisa wannan hali da muke ciki.” In ji Alhaji Abbas sa’id Umar

Shugaban kungiyar ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa amincewa da dawo mana da wani yanki daga wuraren da aka rushe mana.

” Shagunan sun kai 700 da aka rushe, amma cikin ikon Allah gwamnatin jihar Kano ta amince da samar shaguna 75 da Kuma Karin wasu a nan gaba ga mutanen mu domin ciga da kasuwancin su.” In ji Shugaban kungiyar

Da yake Karin haske yayin taron, Farfesa Ibrahim Mu’azzam Mai Bushra ya yaba wa gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan halin tausayi ga wadannan masu shaguna da aka rushe wa shagunan su shekaru 3 da suka gabata.

Shi ma Farfesa Ibrahim Ahmad Muhammad na Jami’ar Tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya bayyana sake Samar wa da ‘yan Kasuwar ta filin Idi da cewa zai kara inganta sha’anin kasuwancin jihar Kano da ma kasa baki Daya.

Continue Reading

Labarai

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kano

Published

on

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Filin Idi Ta Yi Taron Addu’oi Na Musamman Ga Gwamna Abba Da Sarkin Kan

Trending